(MATAWALLE NEW MEDIA PROMOTERS) (MNMP).
FASSARAWA........
GYERAN TAKAMAMMEN ILIMIN JAHAR ZAMFARA:GOV MATAWALLE YA KADDAMARDA BADA KWANGILAR GINA AJUJUWAN YANMAKARANTA GUDA 423 A ZAMFARA.
"Mai girma gwamnan jahar zamfara Dr bello muhammed matawallen maradun(BARDEN KASAR HAUSA) yabada kwangilar gina ajujuwan dalibbai guda 423 a jihar ansamu bada wannan kwangilar ne ga kwararrun yankwangila dakuma eginiyoyi "inji gwamna.
Gwamnan ya tabbatar da hakan ne a yayin wani gabatarwa na satifiket din kwangilar zuwa ga: benefiting home based contractors:wanda aka halarta a gidansa na gusau babban birnin jahar.
A lokacinda ake zantawar Gov matawalle yakara bada tabbacin amincin gwamnatinsa akan samarda sabon gyara ga takamammen bangaren ilimin jahar zamfara.
GOV MATAWALLE yayi bayani dacewa tun lokacinda gwamnatinsa tazo,yayi kokarin tabbatarda _{YANAYIN TABACI}, ga bangaren ilimin jahar zamfara saboda shi da ilahirin mutanensa sun yi amanna dacewa shi ilimi yana nan a matsayin kashin bayan cigaban dukkan wata Alkarya dakuma yelwar dukkanin wani tattalin arziki a cikin duniya baki daya.
yakara dacewa gwamnatinsa zata cigaba da bada cikakken mahimmanci ga abunda yashafi bangaren ilimin jahar saannan zai cigaba da amfani da duk wata dama data samu ta hanyar yin gyara a inda waccan tsohuwar gwamnatin ta kasa wanda yakaiga tababarewar arzikin bangaren ilimin jahar.
GOV_MATAWALLE yakara da cewa bayan ginin da za'ayi na ajujuwan guda 423,da akwai ajujuwa 148 wadanda za'a gyara tareda yin pampon ruwa da tankuna domin samar da isasshen ruwa mai kyau ga malamai dakuma dalibban kowace makaranta acikin fadin jahar.
GOV_MATAWALLE yayi kira ga kwararrun ma'aikatan gini dakuma yan kwangila dasuyi aiki tsakaninsu da Allah tareda cika alkawaroran da akayi na kwangilar dakuma tabbatar da yin aiki da sababbin kwararrun kayan gini na zamani masu karko a wurin yin ginin domin amfanin jahar dakuma yaran goben jahar.
Mai daraja gwamna yace yana bada mahimmanci ga dokar gwamnatinsa ta amfani da leburorin jahar domin samar da aiki ga marasa aiki acikin jahar tareda sayen dukkanin wani kayan ginin acikin jahar ta zamfara domin kawo cinaki dakuma bunkasar tattalin arzikin yan kasuwar sannan yakara da cewa dukkanin wani dan kwangila da karya dokar gwamnati to lallai za'a gaggauta korarsa nan take.
acikin bayaninsa_chairman na zamfara state universal basic education board(ZSUBEB) Honourable abubakar aliyu{DANMADAMIN MARADUN} yace kwangilar gina ajujuwan guda 423 na dalibbai tana karkashin matching grant na 3.1billion naira sa'annan bayan wadannan ajujuwan guda 423 da akwai wasu guda 148 wadanda za'a gyara,pampon bohol19 tareda tankunansu na ruwa,aikin zagaye makarantu 20,dakuna57 na toilet tareda kashi ukku(3) na makewayi.
Dan madamin maradun ya bayyana cewar dukkanin kwangilolin da aka bayar ta karkashin ma'aikatarsa a karkashin grants intervension na 2018 wanda yakeda kudi 5.5billion naira an kammalasu.
Chairman din yayi bayani akan cewar sama da ajujuwa guda 900 ne aka gina kawo yanzu,sannan lalatattun aji guda 375 ne aka gyara acikin jahar.
sa'annan yamika godiyarsa zuwaga mai girma gwamna abisa giyon baya dakuma tallafi wanda ya baiwa ma'aikatar tasa.
Babban bikin yasamu halartar mataimakin gwamna,Barr mahdi Aliyu gusau,dakuma shugaban ma'aikatan gidan gwamnati,col Bala mande rtd,commissioner na manyan ayukka dakuma labarai,muhammad maiturare sadiq dakuma suleiman tunua anka da sauransu.
Sign
Amßassador Basheer Isah Gusau
State Coordinator MATAWALLE NEW MEDIA PROMOTERS
Comments
Post a Comment