YADDA JIHAR ZAMFARA TA SAMU GAGARUMIN CIGABA CIKIN HANZARI A ZAMANIN MAI GIRMA GWAMNA HE BELLO MATAWALLE (MON).
Daga: MATAWALLE NEW MEDIA PROMOTERS
Mun Yi Ƙoƙarin Fito Da Wasu Ayyuka Daga Cikin Ɗumbin Ayyukan Da Mai Girma Gwamna, HE Bello Matawalle Ya Yi A Jihar Zamfara, Kuma Na Tabbata Ko Maƙiyan Mai Girma Gwamna HE Bello Matawalle Ba Za Su Iya Ƙaryata Wannan Cigaban Da Ake Samu Ba, Sai Dai Ƙiyaya Ta Hana Su Faɗa.
Yau Attanin, 18 ga watan mayun, 2020. Domin ƙara shaidawa Duniya yadda Jihar Zamfara ke cigaba da bunƙasa ta fannoni daban-daban a zamanin mai girma gwamna Dakta Bello Matawalle, Kungiyar MATAWALLE NEW MEDIA PROMOTERS, Ta yi ƙoƙarin fito muku da Wasu ayyukansa daga cikin ɗumbin ayyukan da ya yi a zangon mulkinsa na farko dake gudana a Yanzu.
A ƙoƙarinsa na kyautata walwala da jindaɗin al'ummar Jihar Zamfara a fannoni daban-daban na rayuwar ɗan adam, a 2019, majalissar zartarwa ta Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamnan Jihar Zamfara, HE BelloMatawalle, ta amince da fitar, gami da kashe zunzurutun kuɗi, Domin gudanar da aikin gyaran wasu tituna na cikin Jihar Zamfara.
Daga cikin titunan da majalissar zartarwar ta amince a fitar da waɗannan kuɗaɗe domin a gyara su, sun haɗa da:
-Titin Anguwar Nassarawa zuwa Gadar Abu Magaji.
-Sabunta Titin kantin daji dake Garin Gusau
-Da kuma titin Wurin Gidan Galadiman Gusau, Daura da masallacin Jumma'ah Na Gari duka.
-Sai kuma titin Daya tashin daga wurin masallacin Jumma'ah Na Yar Bawa zuwa har wurin tankin Ruwa dake Sabon Gari.
Kuma kamar yadda al'umma su ka sani, yanzu haka tuntuni an kammala gyaran titunan.
Bugu da ƙari, a dai-dai wannan lokaci, bayan kuɗaɗen aikin gyaran waɗannan hanyoyi da majalissar zartarwar Jihar Zamfara, ƙarƙaahin jagorancin mai girma gwamna, HE BelloMatawalle ta amince a fitar kan waɗancan ayyuka, ta kuma sake amincewa da fidda wasu makudan kuɗaɗen domin sabunta wasu hanyoya a jihar Zamfara.
Daga wancan lokaci zuwa yau, duk waɗannan ƙudurori na gyaran hanyoyi da samar da Wuraren samun Kudin Shiga, da kuma ciyar da ɗalibai ƴan makarantun firamare, duk sun tabbata, abubun kuma da ba su kai ga kammaluwa ba, su ma ana daf! Da kammala su.
Gwamna Bello Matawalle, ya samu nasarar kammala wani katafaren Asibitin kula da Masu dauke da Cutar Covid-19 (CoronaViros) da ke ƙaramar hukumar Gusau a shiyar Damba, a kan titin zuwa Tsafe, Zaria to Kaduna. Kuma mai girma gwamna ya samar masa da kayan aiki irin na zamani domin ganin an kula da lafiyar Al'ummar Jihar Zamfara.
Gwamna Bello Matawalle, ya samu nasarar Gina Katafariyar Asibitin da Katafariyar Makaranta a garin Maradun, Wanda Har Yanzu bamu samu Labarin sunan da aka sakama Sabbin gine-ginen ba da ke ƙaramar hukumar Maradun.
Haka zalika Mai Girma Gwamna HE BelloMatawalle ya gina primary health a garin anka guda biyu.
A Karamar hukumar Kaurar Namoda Mai Daraja gwamnan HE BelloMatawalle ya gina makarantun Boko primary school a Galadima D/Galadima ward (Magizawa) Kaura Namoda.
Insha Allah Rabbi zamuci Gaba da kawo maku kyawawan ayukkan Matawalle Maradun, domin al'ummar wannan jiha su banbance tsakanin aya da tsakkuwa, Kuma zaku tsayu akan Kare martabar wannan Gwamnati da hujjoja kwarara.
Tsarawa da Gabatarwa.
State Coordinator Matawalle New Media Promoters
Ambassador Basheer Isah Gusau
18/05/2020

Comments
Post a Comment